Kungiyar cinikayya ta duniya (WTO) ta gudanar da taron tattaunawa kan tallafa wa cinikayya karo na 64 a birnin Geneva na Switzerland jiya Alhamis. A yayin taron, wakilin kasar Sin ya bayyana nasarorin da Sin ta samu wajen ba da taimakon fasahar noma ga Afirka, wanda ya samu yabo sosai daga dukkan mahalarta taron.
Wakilin kasar Sin ya yi bayanin cewa, shekaru da dama da suka wuce, Sin ta baiwa kasashe Afirka fiye da 30 tallafin noma mai lakabin “kanana ne amma masu kyau”, alal misali, yayata amfani da fasahar noman shinkafa mai aure da Sin ta kirkiro a Burundi, da kafa cibiyar nuna fasahar kiwo a Muritaniya, da aiwatar da ayyukan samar da kayayyakin aiki na kula da nazarin yanayi a kasashe sama da goma kamar Habasha, da sauransu. Wadannan ayyukan sun ba da gudunmawar fasaha, gogewa da tsare-tsare na kasar Sin ga ci gaban noma da samar da isasshen abinci a Afirka.
Wakilai kusan 100 na mambobin WTO sun yi magana, inda suka yaba da irin gudunmawar da kasar Sin ta bayar wajen taimakawa kasashen Afirka domin tabbatar da samun isasshen abinci. Wakilin kasar Cadi wanda ke wakiltar kungiyar Afirka ya bayyana cewa, taimakon noma da Sin ke bai wa Afirka wani muhimmin bangare ne na kawancen Sin da Afirka, kuma yana taimakawa wajen sauya tsarin nahiyar Afirka da hadakar tattalin arziki.
Kazalika, wakilin Gambia wanda ke wakiltar rukunin kasashe masu karancin ci gaba ya bayyana cewa, taimakon noma da Sin ke bai wa Afirka ya yi tasiri mai zurfi, inda ya haifar da karuwar yawan amfanin gona da kuma kudin shigar manoma a Afirka. (Amina Xu)














