• English
  • Business News
Sunday, August 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wurin Da Ya Fi Ba Ni Wahala A Daukar Shirin Labarina – Hadiza Abubakar

by Sulaiman and Rabilu Sanusi Bena
1 year ago
in Nishadi
0
Hadiza Abubakar
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A yau ma shafin namu ya yi tozali da wata matashiyar Jarumar mai haskawa cikin masana’antar Kannywood wato, HADIZA ABUBAKAR wacce aka fi sani da UMMI GOMBE. Ta bayyana wa masu karatu yadda aka yi har ta tsinci kanta cikin masana’antar Kannywood, tare da yin kira da ba da shawarwari ga masu kokarin shiga cikin masana’antar tare da sauran abokan sana’arta har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Da farko za ki fada wa masu karatu cikakken sunanki tare da sunan da aka fi saninki da shi.

Sunana Hadiza Abubakar wacce aka fi sani da Ummi Gombe.

 

Ko za ki iya fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

Labarai Masu Nasaba

Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya

Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu

Kamar yadda na fada a baya sunana Hadiza Abubakar wacce aka fi sani da Ummi Gombe, an haife ni a Kumo Jihar Gombe, kuma na tashi a garin Gombe.

 

A wanne mataki kika tsaya a karatunki?

Na tsaya da karatuna a matakin Sakandare.

 

Ya batun komawa makaranta dan ci gaba da karatu, shin akwai ra’ayin hakan ko babu?

Ina nan ina shiri yanzu haka ma abin da nake kokarin yi kenan.

 

Kin taba yin aure ko tukunna dai?

Eh! Na taba yin aure.

 

Akwai yara ko babu?

Ina da yaro guda daya.

 

Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?

Abin da ya ja hankalina gaskiya ni dai na taso da sha’awar abun ne tun ina karama.

 

Wane rawa ki ke takawa a cikin masana’antar Kannywood?

Ina taka rawar matsayin jaruma.

Hadiza Abubakar

Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance?

An sha gwagwarmaya sosai gaskiya.

 

Lokacin da ki ka fara sanar da iyayenki kina son fara harkar fim, shin kin fuskanci wani kalubale daga gare su ko kuwa?

Ban samu wani kalubale daga gare su sosai ba, addu’a kawai suka yi mun.

 

Za ki yi kamar shekara nawa ko wata nawa da fara fim?

Eh! To, ba zai wuce kamar shekara takwas ba.

 

Da wane fim ki ka fara?

Na fara fitowa a fim din Wuta Biyu.

 

Ya farkon farawar ya kasance?

Kin san duk abin da aka ce farko ne to dole akwai faduwar gaba.

 

Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?

Nayi finafinai masu dan yawa ciki akwai; Bikin Suna, Zabi, da dai sauransu, sannan a yanzu ina daya daga cikin jaruman shiri me dogon zango na Labarina.

 

Wace rawa ki ka taka a cikin shirin Labarina?

Na fito a Yasmeen kawar Maryam.

Hadiza Abubakar

Ta ya kika tsinci kanki a cikin shirin Labarina?

Ina daune Darakta Aminu Saira ya sa aka kira ni aka ce an yi ‘casting’ dina a fim din Labarina.

 

Cikin finafinan da ki ka fito ciki, wanne ne ya zamo bakandamiyarki?

Kowanne amma ina son Labarina.

 

Wane waje ne ya fi burge ki a cikin shirin Labarina?

Wajen da kawata Safina ta sammun Dalar da ta samo.

 

Ko akwai wani waje da ya fi baki wahala cikin finafinan da ki ka fito wanda ba za ki iya mantawa da shi ba?

A cikin shirin Labarina wajen da muka kai Maryam muka fito bayan na sha aiki sai jiri ya biyo baya ga kuma gajiyar aikin da muka gama.

 

Kamar wane irin nasarori kika samu game da fim?

Gaskiya Alhmdulillah na samu nasarori da yawa.

 

Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta cikin masana’antar bayan shigarki?

Ba za a rasa ba tunda a rayuwa ba a rasa kalubale, sai dai na ce Alhamdulillah.

 

Kina da Ubangida a cikin masana’antar Kannywood?

Duk wanda ya taba sani ko niyyar sani ubangidana ne.

 

Wadanne jarumai ne suke burge ki kafin ki fara fim?

Shi fim din ne yake burge ni.

 

Mene ne burinki na gaba game da fim?

Burina shi ne nayi shuhra bayan haka kuma sai aure.

 

Ko akwai wanda ya taba cewa yana son ki cikin masana’antar da har ta kai da kun fara soyayya?

Eh! To, ba za a rasa ba.

 

Kamar wane irin namiji ki ke son aura?

Wanda Allah ya zaba min tunda ba lalle wanda kake so ya zama mafi alkairi a tare da kai ba.

Hadiza Abubakar

Bayan fim kina wata sana’ar ne?

Eh! Ina siyar da kayayyaki kamar su; Atampha, Takalma da sauransu.

 

Ko akwai wani kira da za ki yi ga sauran abokan aikinki?

Ina kira gare su da mu kara hada kanmu mu zama tsintsiya madaurinki daya.

 

Wane irin kira za ki yi ga masu kokarin shiga cikin masana’antar Kannywood?

Kira na ga masu sha’awar shiga masana’antar Kannywood su tabbata da izinin iyayensu za su shiga.

 

Me za ki ce da masoyanki?

Ina yi musu godiya Allah ya bar mu tare kuma idan nayi kuskure su yi kokarin nusar da ni ta yadda zan fahimta.

 

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Ina gaida duk masoyana.

 


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Adon GariKannywoodYan matan Film
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ba Zan Taba Mantawa Da Zamowata Gwarzuwar Banki Sau Biyu A Jere Ba – Fatima Gana

Next Post

Shugaba Bola Tinubu Zai Yi Sauye-Sauye A Gwamnatinsa  Kwanan nan

Related

Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya
Nishadi

Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya

7 days ago
Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu
Nishadi

Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu

2 weeks ago
Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya
Nishadi

Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya

2 weeks ago
An Ɗaura Auren Rahma Sadau A Kaduna
Nishadi

An Ɗaura Auren Rahma Sadau A Kaduna

2 weeks ago
Samun Kuɗi Ya Fi Samun Ɗaukaka Wahala A Kannywood -Baba Sadiƙ
Nishadi

Samun Kuɗi Ya Fi Samun Ɗaukaka Wahala A Kannywood -Baba Sadiƙ

3 weeks ago
Ban Yi Danasanin Shiga Harkar Fim Ba – Baba Ƙarami
Nishadi

Ban Yi Danasanin Shiga Harkar Fim Ba – Baba Ƙarami

3 weeks ago
Next Post
Shugaba Bola Tinubu Zai Yi Sauye-Sauye A Gwamnatinsa  Kwanan nan

Shugaba Bola Tinubu Zai Yi Sauye-Sauye A Gwamnatinsa  Kwanan nan

LABARAI MASU NASABA

NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru

NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru

August 23, 2025
Amfani Da Rashin Amfanin Auren Jari

Amfani Da Rashin Amfanin Auren Jari

August 23, 2025
CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu

CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu

August 23, 2025
Yadda Ake Alale

Yadda Ake Alale

August 23, 2025
Babban Sakataren SCO: Sin Na Taka Rawar Gani A Matsayin Kasar Da Ke Shugabancin SCO

Babban Sakataren SCO: Sin Na Taka Rawar Gani A Matsayin Kasar Da Ke Shugabancin SCO

August 23, 2025
Matsalar Al’ada Da Ciwon Mara Ga Mata

Matsalar Al’ada Da Ciwon Mara Ga Mata

August 23, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Gangamin Tattara Fina-Finai Da Talabijin Da Aka Samar Bisa AI A Los Angeles

CMG Ya Kaddamar Da Gangamin Tattara Fina-Finai Da Talabijin Da Aka Samar Bisa AI A Los Angeles

August 23, 2025
Taron Kare Hakkin Dan Adam Na Sin Da Afirka Na Farko Ya Nemi Hada Karfi Don Tabbatar Da ‘Yancin Samun Ci Gaba

Taron Kare Hakkin Dan Adam Na Sin Da Afirka Na Farko Ya Nemi Hada Karfi Don Tabbatar Da ‘Yancin Samun Ci Gaba

August 23, 2025
Bangaren Kasuwancin “E-Commerce” Na Kasar Sin Ya Karu Sosai A Watanni 7 Na Farkon Bana

Bangaren Kasuwancin “E-Commerce” Na Kasar Sin Ya Karu Sosai A Watanni 7 Na Farkon Bana

August 23, 2025
Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

August 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.