Akalla mutane 18 ne suka mutu sakamakon fashewar wani abu a wata haramtacciyar matatar mai a yankin Ibaa da ke karamar hukumar Emuoha a Jihar Ribas.
Leadership Hausa ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi lokacin da wasu jama’a ke diban man fetur.
- Tallafin Fetur: Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Abinci
- Kotun Zaben Kano: DSS Ta Cafke Matar Da Ta Yi Wa Shettima, Gawuna Da Alkalin Kotun Barazana
Wata majiya a yankin ta ce fashewar ta afku ne a lokacin da daya daga cikin kwantenar da za a yi amfani da su wajen tace danyen mai ta kama da wuta.
Ya ce jama’a ba za su iya tantance adadin wadanda suka mutu ba, amma ana kyautata zaton mutane da dama sun mutu a wurin.
Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, inda ta ce mutane 18 ne suka mutu a lamarin.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NSCDC, Olufemi Ayodele ya fitar, ya ce wadanda abin ya shafa sun kone kurmus.
Ya bayyana cewa an ceto wasu 25 da raunuka, ya kara da cewa binciken farko ya nuna cewa wurin mallakar wani mutum mai suna John Bodo ne wanda shi ma ya samu mummunan rauni, yayin da dansa, Uche John Bodo, wanda ya kammala karatun digiri ya mutu nan take.
NSCDC ta bayyana sauran wadanda abin ya shafa da mata masu juna biyu da wata budurwa da ake aurenta a wata mai zuwa.