• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Da Takwaransa Na Togo Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Huldar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu

by CMG Hausa
3 years ago
Togo

A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Togo Faure Essozimna, suka aikewa juna sakon taya murnar cika shekaru 50, da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashensu, inda cikin sakon sa shugaba Xi ya bayyana cewa, akwai dadadden zumuncin gargajiya tsakanin Sin da Togo, kuma duk da cewa, yanayin duniya yana sassauyawa a cikin shekaru 50 da suka gabata, amma a ko da yaushe sassan biyu na ci gaba da goyawa juna baya, kan batutuwan dake shafar babbar moriyarsu, da al’amuran dake jawo hankalinsu, don haka hadin gwiwar dake tsakaninsu ya samu babban sakamako, ta yadda yake amfanar al’ummun kasashen biyu baki daya. 

Ya ce yanzu haka ana fuskantar matsalar yaduwar annobar cutar COVID-19 a fadin duniya, don haka ya dace al’ummun kasashen biyu su kara hada kai domin dakile annobar, tare kuma da kara zurfafa zumuncin dake tsakaninsu yadda ya kamata.

  • Xi Jinping Ya Yi Ziyarar Aiki A Uzbekistan Tare Da Halartar Taron SCO

Shugaba Xi ya kara da cewa, yana mai da hankali matuka kan ci gaban huldar dake tsakanin kasarsa da kasar Togo, yana kuma son yin kokari tare da takwaransa na kasar Faure Essozimna, a yayin da ake taya juna murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya dake tsakanin kasashen biyu, domin kara karfafa amincin siyasa, da hadin gwiwa a fannoni daban daban tsakaninsu, tare kuma da ciyar da huldar sassan biyu gaba, da taka rawa a fannin gina kyakkyawar makomar al’ummun Sin da Afirka bai daya.

A nasa bangare, shugaba Faure ya yi tsokaci da cewa, har kullum kasar Sin aminiyar kasar Togo ce, yayin da take kokarin raya kan ta, kuma yana farin cikin ganin yadda kasar Sin din ke yin kokari tare da kasashen Afirka, wajen kara karfafa huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka, ta yadda za su samu wadata tare.

Ya kara da cewa, kasar Togo tana nacewa, kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, yana kuma son yin kokari tare da shugaba Xi, wajen ciyar da huldar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin gaba yadda ya kamata. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)

LABARAI MASU NASABA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Daga Birnin Sin

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
Daga Birnin Sin

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Daga Birnin Sin

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Next Post
NIS

NIS Na Horar Da Jami’anta Na Hulɗa Da Jama’a Kan Dabarun Aiki Na Zamani

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

November 1, 2025
Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

November 1, 2025
An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.