Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, alakar kasarsa da Brazil ta kai wani muhimmin mataki a tarihi, inda ake dorawa kan irin ci gaban da aka samu a baya, tare da tunkarar sabbin nasarori, a gabar da Sin da Brazil din ke bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya a wannan shekara ta 2024.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi cikin wata rubutacciyar sanarwar da aka fitar, yayin da ya isa birnin Rio de Janeiro, don halartar taron kolin kungiyar G20 karo na 19, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar Brazil. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp