A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da babbar gwamnar New Zealand Cindy Kiro, suka yi musayar sakwannin taya murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen su.
A cikin sakon da ya aike, shugaba Xi ya ce cikin shekarun nan 50 da suka gabata, alakar kasashen biyu ta ci gaba da gudana lami lafiya, tare da samun ci gaba, yayin da kuma aka rika kulla sabbin hadin gwiwa a fannoni masu yawa tsakanin kasashen biyu, matakin da ya yi matukar amfanar al’ummun su, tare da ba da gudummawa ga zaman lafiya da wadata, da daidaito a yankunan da suke.
Shugaba Xi ya ce yana dora muhimmancin gaske, kan manufar bunkasa alakar dake tsakanin kasar sa da New Zealand, kuma a shirye yake da ya yi aiki tare da uwargida Kiro, ta yadda za su kididdige tarihin nasarorin sassan biyu, da karfafa tattaunawa da juna, da ingiza cikakken hadin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare, domin samar da karin moriya ga al’ummun kasahen biyu.
A nata bangare kuwa, Kiro ta ce New Zealand na matukar martaba musaya ta tsawon tarihi da sassan biyu ke yi, tana kuma fatan ci gaba da yayata hadin gwiwar kasashen biyu, ta yadda hakan zai amfani al’ummun kasashe biyu da ma dukkanin duniya baki daya. (Saminu Alhassan)