A daren yau 31 ga watan Agusta, Shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan sun shirya liyafar maraba a cibiyar baje kolin kayayyaki ta Meijiang da ke Tianjin, don maraba da baki na kasa da kasa wadanda suka zo nan kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin kan Shanghai (SCO) na shekarar 2025.
A cikin jawabin gaisuwar, Xi Jinping ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kafa kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO), ta kasance tana rike da “Ruhin Shanghai,” tana karfafa hadin kai da amincewa da juna, da kara zurfafa hadin gwiwa, kana da shiga cikin al’amuran kasa da kasa da na yanki, ta zama wata muhimmin karfi wajen inganta sabuwar dangantakar kasa da kasa da kuma gina kyakkyawar makomar bil’adama ta bai daya.
A halin yanzu, ana fuskantar sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu a shekaru dari da suka gabata ba, halin rashin kwanciyar hankali, rashin tabbas, da kuma wahalhalu sun kara karuwa. Kungiyar SCO tana da babban alhakin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da kuma habaka ci gaban da wadatar kasashe.
Shugaba Xi ya yi imanin cewa, kungiyar SCO za ta ba da karin gudunmawa wajen samun ci gaba, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe membobinta, da tara karfin kasashe masu tasowa, da kuma taimaka wa ci gaban wayewar kan dan Adam, a karkashin hadin gwiwa na dukkan bangarori.
Kafin liyafar maraba, Shugaba Xi da madam Peng Liyuan sun yi maraba da shugabannin kasashen waje da matansu cikin fara’a, inda suka mika musu hannu tare da gaisawa, kuma suka dauki hotuna tare da su.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp