A jiya Talata kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ya wallafa wani dogon bayani mai taken “Xi Jinping jagoran sabon tafarkin kasar Sin”, inda aka rubuta abubuwa da dama da suka shafi bayanin aiki da kuma rayuwarsa, da kuma bayani kan tunaninsa na tafiyar da harkokin kasa.
Abubuwan da aka rubuta sun hada tarihin yadda ya girma, da tarbiyar iyalinsa, da tarihin aikinsa, da nasarorin da ya cimma a aikinsa, da sauransu.
A cewar bayanin, a matsayinsa na babban sakataren kwamitin kolin JKS, Xi Jinping yana alfaharin kara karfin jamhuriyar jama’ar kasar Sin, ya kuma dukufa kan babban aikin yin kwaskwarima da bude kofa ga ketare, ta hanyar tsara shirin raya kasa mai dorewa, abin da ya sa shi samun karbuwa matuka daga al’ummun Sinawa, haka kuma masu nazarin harkokin siyasa na kasashen ketare da manyan jami’an siyasar kasa da kasa suna yaba masa matuka. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)