Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da shugaban janhuriyar dimokuradiyyar Congo Felix Tshisekedi Tshilombo, wanda ke ziyarar aiki yanzu haka a kasar Sin.
Yayin zantawar ta su a juma’ar nan, shugabannin biyu sun bayyana daga matsayin dangantakar kasashen su, daga dangantakar kawance ta hadin gwiwar cimma moriyar juna, zuwa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni.
Da yake tsokaci kan hakan, shugaba Xi Jinping ya ce kasar sa a shirye take ta karfafa dukkanin matakan wanzar da ci gaba tare da janhuriyar dimokaradiyyar Congo, da tallafawa juna, da lalubo hanyoyin hadin gwiwa, da ingiza bunkasuwa, da kara samar da ci gaba tare, kan hanyar cimma nasarori da farfadowa. Shugaba Xi ya ce ya yi imanin cewa, ci gaba mai inganci da Sin ta samu, zai samar da karin damammakin hadin gwiwa, da fadada kasuwa tare da kasar Congo, da kuma ingiza karin ci gaban alakar sassan.
A nasa tsokaci kuwa, shugaba Tshisekedi cewa ya yi zai yi amfani da wannan dama, wajen jinjinawa dimbin nasarori da kasar Sin ta cimma a tsawon shekaru 10 na sabon zamanin nan, musamman ma matakan kasar na zamanantar da kai masu matukar ban mamaki. Daga nan sai ya bayyana hasashen sa, na ganin Sin ta cimma burinta na zama kasar gurguzu mai karfin ci gaban zamani ya zuwa shekara ta 2049, wato lokacin cikar kasar shekaru 100 da kafuwa.
Bayan tattaunawar, shugabannin 2 sun kuma kalli yadda aka sanya hannu kan takardun hadin gwiwar kasashen su a fannin zuba jari, da bunkasa tattalin arziki maras gurbata yanayi, da tattalin arziki ta amfani da fasahohin zamani. (Saminu Alhassan)