Da safiyar yau Alhamis 30 ga watan nan na Oktoba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Busan na Koriya ta Kudu.
Yayin tattaunawar Xi ya bayyana cewa, shugaba Trump yana da himma wajen magance muhimman matsalolin dake janyo hankali, kuma kasar Sin tana ci gaba da yin kokari bisa hanyoyi irin nata don samar da sulhu, da tattaunawa kan matsalolin da ke faruwa a yanzu. Ya ce har yanzu akwai matsaloli da yawa a duniya, kuma Sin da Amurka za su iya sauke nauyin dake wuyansu na manyan kasashe cikin hadin gwiwa, don cimma manyan ayyuka masu amfani ga kasashen biyu da sauran sassan duniya.
Xi ya jaddada cewa, ci gaban kasar Sin da kuma burin shugaba Trump, na “Sake wadatar da Amurka da samun ingantaccen ci gaba” ba su ci karo da juna ba, kuma kasashen biyu na iya samun ci gaba tare da bunkasa tattalin arzikinsu. Ya kuma yi fatan hada kai da shugaba Trump, don kafa tushe mai karfi na dangantakar kasashen biyu, da kuma samar da kyakkyawan yanayin ci gaban kasashen biyu.
Xi ya kuma bayyana cewa, saboda bambancin yanayin kasashen Sin da Amurka, ba makawa akwai wasu sabanin ra’ayi, amma baya ga kalubale da takara, ya kamata shugabannin biyu su rike shugabanci, da kuma samar da alkibla mai dacewa, don ba da damar bunkasa dangantakar Sin da Amurka ta ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali.
A nasa bangare, Trump ya ce, yana farin ciki matuka bisa haduwa da dadadden abokinsa. Ya ce, “Za mu tattauna da mai girma shugaban kasar Sin Xi Jinping. Ina da imanin cewa, mun riga mun kai ga cimma matsaya daya, kuma za mu cimma karin matsaya a nan gaba. Xi Jinping wani sahihin shugaba ne mai kima.”
Ya kuma ce, “Ba shakka kasashen biyu za su kafa nagartacciyar hulda ta dogon lokaci, ina kuma farin cikin hakan tare da shugaba Xi.”
Shugabannin biyu sun shafe sa’a 1 da mintuna 40 suna tattaunwa.
A wannan rana kuma, shugaban kasar Xi Jinping ya isa kasar Korea ta Kudu, domin halartar taron kwarya-kwarya na shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Asia da Pasifik (APEC) karo na 32, bisa gayyatar da shugaban kasar Korea ta Kudu Lee Jae-myung ya yi masa.(Amina Xu)
 
			




 
							








