• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping: Sin Na Goyon Bayan Shigar Da Kungiyar AU G20

by Sulaiman and CMG Hausa
3 years ago

Da safiyar yau Talata ne aka bude zaman farko na taron kolin G20, a tsibirin Bali na kasar Indonesiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron, ya kuma gabatar da jawabi.

A jawabin nasa Xi Jinping ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar babban kalubalen raya kasashen duniya. Don haka ya kamata mambobin G20 su sauke nauyin dake bisa wuyansu a matsayinsu na manyan kasashen duniya, domin neman bunkasuwar kasa da kasa, da tallafawa alummun duniya, yayin da ake tabbatar da ci gaban duniya baki daya.

Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu, kasashen duniya, musamman ma kasashe masu tasowa suna fuskantar kalubalen raguwar tattalin arziki.

Don haka ya ba da shawarar kafa dangantakar abokantaka ta neman farfado da tattalin arzikin duniya, da mai da aikin neman ci gaba, da raya alumma a matsayin babban aikin da aka sanya gaba, tare da mai da hankali kan bukatun kasashe maso tasowa. Kaza lika ya ce kasar Sin tana goyon bayan shigar da kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU kungiyar G20.

Haka kuma, cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, a halin yanzu, ya kamata a nemi ci gaban da kowace kasa za ta iya cin gajiya.

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Ci gaban da kowace kasa za ta ci gajiya tare, hakikanin ci gaba ne da ake bukata. Ya kamata kasashen dake kan gaba wajen samun ci gaba, su ba da taimako yadda ya kamata ga sauran kasashe, da kuma samar musu karin damammakin da suke bukata.

Ya ce, Kalubaloli masu tsanani da ake fuskanta wajen neman bunkasuwar kasashen duniya, su ne babu isashen hatsi da makamashi. Kuma, muhimmiyar hanyar da za mu yi amfani da ita wajen shawo kan wadannan kalubaloli ita ce, yin hadin gwiwa kan aikin sa ido a kasuwanni, da kuma kafa manyan kasuwannin bude kofa ga waje, domin karfafa tsarin samar da kayayyaki cikin hadin gwiwa, da kuma daidaita farashin kayayyaki yadda ya kamata.

Bugu da kari, Xi Jinping ya ce, a yayin babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin karo na 20 da aka yi watan jiya, an tabbatar da burin ci gaban kasar Sin da na JKS cikin shekaru 5 masu zuwa.

Kuma kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen neman bunkasuwa cikin lumana, da zurfafa aikin kwaskwarima, da kuma kara bude kofa ga waje, domin neman farfadowar kasar Sin baki daya ta hanyar zamanintar da kasar. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai
Daga Birnin Sin

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya
Daga Birnin Sin

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%
Daga Birnin Sin

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Next Post
Osinbajo Bai Halarci Taron Yakin Neman Zaben APC A Filato Ba

Osinbajo Bai Halarci Taron Yakin Neman Zaben APC A Filato Ba

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.