Yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aika da sako ga taro na 38 na kungiyar Tarayyar Afrika (AU), yana mai taya kasashen nahiyar da al’ummominsu murna.
Ya ce duk da yanayi na sarkakiya da duniya ke ciki, kasashe masu tasowa da Sin da Afrika ke wakilta, sun samu ci gaba sosai.
Ya kara da cewa, cikin shekarar da ta gabata, AU ta jagoranta tare da hada kan kasashen Afrika ga dunkulewa, da kuma tunkarar kalubalen yankuna da ma na duniya, inda take magana da muryar daukacin nahiyar.
Shugaban na Sin ya ce shekarar 2024, ta kawo gaggarumin ci gaba a hadin gwiwar Sin da Afrika. Kuma bisa nasarar taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika, bangarorin biyu sun shiga wani sabon matakin gina al’umma mai makoma ta bai daya da za ta iya jure kowanne yanayi.
Bugu da kari, Xi Jinping ya bayyana shirinsa na hada hannu da shugabannin nahiyar wajen aiwatar da shawarwari 6 na bunkasa zamanantarwa da ayyukan hadin gwiwa 10, ta yadda za a kara samun kwararan sakamakon da za su amfanawa al’ummun Sin da Afrika da yawansu ya kai biliyan 2.8.
A yau Asabar ne aka bude taron shugabannin kasashe da gwamnatocin AU a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababa na Habasha. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)