Ba a cika bai wa noman Agwaluma muhimmanci kamar yadda ake bai wa sauran amfanin gonar da ake shuka a Nijeriya ba.
 A yaren Yarbanci, ana kiran ta da Agbalumo, da Iyamuranci; ana kiran ta da Udara, a Jihar Edo; ana kiran ta Otien, inda a yaran Hausa kuma ake kiran ta da Agwaluma.
- Gwamnatin Tarayya Ta Samar Da Rumbun Adana Bayanai Don Tallafa Wa Manoma
- Gwamnati Na ɗaukar Matakai Don Rage Farashin Abinci Ta Hanyar Zuba Jari A Noma – Minista
Manoman da suka shiga cikin fannin, musamman a Nijeriya, na samar wa da kawunansu kudaden shiga masu yawa, haka a daukacin Nijeriya, babu wani addini da ya haramta yin amfani da ita, haka nan kuma; tana kara samun karbuwa a kasuwannin kasar nan.
Yadda Ake Shuka Irin Agwaluma:
Za ka iya shuka Irin nomanta, inda ake bukatar kada Irin ya wuce tsawon wata hudu, inda a lokacin da za ka yi shukar ake bukatar ka tabbatar da ka yi a lokacin rani.
Har ila yau, nau’in Agwaluma na agbalumo ko kuma na Udara, na bukatar yi masa ban ruwa sosai, musamman don ya yi saurin nuna a cikin kasar noman da aka shuka shi.
Bugu da kari, idan manomi zai sayo Irin nomansa, ya tabbatar da ya sayo a gurin da aka fi sani, musamman don ya samu ingantacce kuma mai lafiya.
Ba Ta Kariya Daga Kamuwa Da kwari Ko Sauran Cututtukan Da Ke Harbin Amfanin Gona:
Ana bukatar manomi ya tabbatar da yana ba ta kariya daga harbin kwari ko cututtukan da ke yi mata illa bayan ana shuka ta, domin irin wadannan cututtukan ko kwarin na iya hana Irinta da aka shuka ruba a cikin kasar noman da aka shuka Irin.
Zuwa Tsawon Wane Lokaci Agwaluma Ke Kammala Girma?
Bayan an shuka Agwaluma, musamman Gona na fara fitar da ‘ya’yanta ne daga shekara biyar zuwa 10, inda kuma ake saran saiwar jikinta, domin adana wa ta fi bukatar yanayin da ya kai ma’unin yanayi daga 60 zuwa 70.
Har ila yau, wasu sun yi hasashen cewa, ba za a iya yin noman Agwaluma a Nijeriya ba, amma maganar ba haka take ba; domin ana iya yin nomanta kuma ta yi kyau sosai har dimbin wacce za a yi hada-hadar kasuwancinta abin da kawai ake bukata shi ne, mayar da hankali kan shuka ta da aka yi da nuna kwarin gwiwa da kuma ba ta kulawar da ta dace.
Abubuwan Da Ya Kamata A Tanada Na Noman Agwaluma Don Samun Riba A Nijeriya
Samar Da Kyakkyawan Tsari:
Kafin ka fara yin nomanta, ka tabbatar ka tsara yadda noman nata zai kasance, musamman domin kaucewa yin asara bayan ka zuba jarinka a ciki.
Gyaran Gonar Shuka Ta:
Kafin ka shuka Irinta, ana bukatar ka tabbatar da kasar noman nata mai kyau ce.
Zabo Nau’in Da Ya Dace:
Na bukatar ka zabo daga cikin nau’ukanta biyu, wato na Udara ko kuma na Agbalumo, inda ake iya gano su ta hanyar girmansu.
Amfanin na kai wa tsawon shekara takwas kafin ta kammala girma, inda kuma aka kara habaka nau’insa wanda zai iya girma bayan shekara uku.
Yadda Ake Girbe Agwaluma:
Akasari, ana girbe ta ne a watan Disamba, sai dai a wannan lokaci, ba ta yin dadi sosai; saboda haka, ana so a bar ta a gonar da aka shuka ta har wani ruwan saman ya kara dukan ta kafin a girbe ta, inda ake yi mata girbin bayan Ganyen ta ya rikide zuwa ruwan dorawa.
Tsara Dabarun Hada-Hadar Kasuwancinta:
Bayan an shuka ta ta girma, za a iya kai ta kasuwa don sayarwa, domin ana nuna ci gaba da batan ta a kasuwa ganin cewa, ana yawan yin amfani da ita. Haka kuma manomi, zai iya wallafa tallan ta a kafar yanar gizo, don masu bukata su gani su kuma saya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp