Yau 10 ga watan Satumba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon taya murnar bude taron hada-hadar ba da hidima ta kasa da kasa na shekara ta 2025.
Xi ya bayyana cewa, a halin yanzu tsarin tattalin arzikin duniya yana fuskantar canje-canje masu zurfi, inda kalubale da damammaki ke tare a wuri guda a bangaren ci gaban duniya. Kasar Sin za ta ci gaba da fadada bude kofar tattalin arziki mai girma, da kuma daidaita ka’idojin kasuwanci na kasa da kasa masu inganci, da kuma gaggauta gwada sabbin hanyoyin kasuwanci a yankunan gwajin ‘yancin kasuwanci da kuma wuraren ba da misali dangane da hada-hadar ba da hidima na kasa, tare da ci gaba da bude kasuwannin ba da hidima bisa tsari, domin karfafa ingancin kasuwanci. Kasar Sin tana fatan hadin gwiwa da sauran kasashe don ci gaba da hadin kai wajen bunkasa hadin gwiwar hada-hadar ba da hidima a duniya, da kuma gina tattalin arzikin duniya mai budaddiyar kofa, domin kara karfin kafa kyakkyawar makomar bil’adama ta bai daya.
An bude taron hada hadar ba da hidima na kasa da kasa na 2025 (CIFTIS) a birnin Beijing a wannan rana, bisa taken “Amfani da fasahar dijital ta zamani don sabunta hada-hadar ba da hidima”, wanda ma’aikatar kasuwanci da gwamnatin birnin Beijing suka shirya tare. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp