A jiya ne, MDD ta gudanar da taron tunawa da ranar goyon bayan Palasdinawa, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aikawa majalisar sakon taya murnar shirya taron.
Xi Jinping ya yi nuni a cikin sakon nasa cewa, batun Palesdinu batu ne mai muhimmanci a yankin gabas ta tsakiya. Kuma daidaita batun Palesdinu cikin adalci a dukkan fannoni, ya shafi zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da kuma yanayin samar da adalci a duniya. Don haka, ya kamata kasashen duniya su tsaya tsayin daka, kan shirin kafa kasashen biyu, da daukar batun Palesdinu a matsayin mai muhimmanci cikin ajandar batutuwa na duniya, don taimakawa Palasdinawa cimma burinsu na gaggauta kafa kasar ta kansu.
Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin tana goyon bayan Palasdinawa da su yi kokarin tabbatar da hakkokinsu ta hanyar yin shawarwari, don samun zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra’ila. Haka kuma kasar Sin za ta ci gaba da samar da gudummawar jin kai, da ta fannin ci gaba, ga Palesdinu don taimaka mata raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama’a.
A matsayinta na kasa mai kujerar din-din-din a kwamitin sulhu na MDD, kana kasar dake kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta, Sin za ta ci gaba da hada kai da ragowar kasashen duniya, don samar da gudummawar shimfida zaman lafiya da tsaro da wadata mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya. (Zainab)