Yau Litinin 4 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga bikin baje kolin sana’o’in zamani na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2023.
A cikin wasikar, Xi ya nuna cewa, kasarsa tana mai da hankali sosai kan bunkasuwar tattalin arziki a fannin fasahar sadarwar zamani, kuma tana ci gaba da sa kaimi ga zurfafa hadin gwiwar fasahohin sadarwar zamani da sassan tattalin arziki dake shafar kayayyaki na zahiri. A cewarsa, Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya wajen kara samun fahimtar sabbin fasahohin sadarwar zamani, da zurfafa mu’amala da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fanni, da sa kaimi ga bunkasuwar sana’o’in zamani, da hanzarta gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ta fannin yanar gizo ta Intanet.
A wannan rana ce aka bude bikin baje kolin sana’o’in zamani na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2023 a birnin Chongqing na kasar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)