A yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murnar cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar cinikayyar Amurka da Sin wato USCBC, inda ya taya kungiyar USCBC da dukkan mambobinta murna, kuma ya mika gaisuwa ga dukkanin wadanda suka dade da mai da hankali da nuna goyon baya ga hadin gwiwar cinikayyar kasashen biyu.
Xi ya bayyana cewa, ba da dadewa ba, ya gana da shugaba Joe Biden a birnin San Francisco, kuma sun yi musayar ra’ayi game da abubuwa masu muhimmanci na ci gaban dangantakar Sin da Amurka, kuma sun cimma muhimmiyar matsaya. Ya ce, bangaren Sin yana bin ka’idojin mutunta juna, da zaman lafiya da juna, ya kamata mu yi aiki tare da kasar Amurka don fahimtar juna, da aiwatar da sakamakon ganawar San Francisco, da inganta ci gaba da kwanciyar hankali don dorewar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka.
- Shugaba Xi Ya Gana Da Manyan Shugabannin Kasar Vietnam
- Xi Ya Yi Kira Da A Zage Damtse Wajen Ba Da Agajin Gaggawa Da Tabbatar Da Samar Wa Jama’a Dumi Da Kwanciyar Hankali A Lokacin Sanyi
Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci ba tare da kakkautawa ba, za ta inganta bude kofa ga waje, da samar da yanayin cinikayya bisa tsarin kasuwanci da dokokin kasa da kasa. Zamanantarwa irin ta kasar Sin za ta kawo karin damammaki ga kamfanonin kasashen duniya daban daban, ciki har da kamfanonin kasar Amurka, akwai manyan damammaki ga karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Amurka, da kuma kyakkyawar makoma. (Safiyah Ma)