A baya bayan nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar malamai da dalibai na cibiyar Conficius dake kwalejin fasaha ta Durban na kasar Afrika ta Kudu, inda ya karfafa musu gwiwar koyon Sinanci yadda ya kamata da bayar da gudunmawa wajen gado da raya abotar dake tsakanin Sin da Afrika ta Kudu da yayata hadin gwiwa da abotar dake tsakanin Sin da Afrika.
Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin da Afrika ta kudu muhimman kasashe ne masu tasowa, kuma kasashen biyu na da dangantakar abota da ’yan uwantaka ta musamman, ya ce koyon yadda harsunan da al’adun juna, zai taimaka wajen inganta fahimtar juna da abota tsakanin al’ummominsu. Ya kuma bukaci su kasance jakadun da za su yi gado tare da raya abota tsakaninn kasashen biyu da bayar da gudunmuwarsu ga inganta abota da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika da gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama.
A watan Maris na shekarar 2013, yayin ziyararsa a Afrika ta kudu, Xi Jinping ya shaida rattaba hannu kan yarjejeniya tsakanin Sin da Afrika ta Kudu kan ginin cibiyar Confucius a kwalejin fasaha ta Durban. A baya bayan nan ne kuma, malamai da dalibai 50 daga cibiyar suka rubuta wasika cikin hadin gwiwa ga Xi Jinping, inda suka bayyana yanayin da suke ciki da nasarorin da suka samu da kuma ra’ayoyinsu game da koyon Sinanci. (Fa’iza Mustapha)