Jiya Lahadi da karfe 4 da minti 40 a rana, bisa agogon wurin, wasu jiragen ruwa 2 masu dauke da ‘yan yawon shakatawa sun kife a wani kogi dake garin Qianxi na lardin Guizhou na kasar Sin, sakamakon kadawar iska mai karfi ba zato ba tsammani, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 10.
Sauran mutane 70 suna kwance a asibiti yanzu, bayan da aka kwaso su daga cikin ruwa, kuma rayukansu ba sa cikin hadari. Ban da haka, akwai wasu mutane 4 da aka ceto, wadanda ba su ji rauni ba.
Bayan abkuwar hadarin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umarni ga hukumomi daban daban, don su yi iyakacin kokarin nemo mutanen da suka fada cikin ruwan, da kubutar da su, da kula da wadanda suka ji rauni, da iyalan wadanda suka rasa rayuka, yadda ya kamata. Haka zalika, ya bukaci gwamnatoci na wurare daban daban na kasar da su dauki darasi daga abkuwar hadarin, da kokarin sauke nauyin dake wuyansu don tabbatar da tsaron al’umma. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp