A ranar Litinin din nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa babu wani takamaimen rikici na nuna son kai da ke wanzuwa a tsakanin kasarsa da kasar Australia.
Xi ya bayyana haka ne a yayin da yake ganawa da firaministan kasar Australia Anthony Albanese, a gefen taron koli na kasashen G20 a birnin Rio de Janeiro.
- Kasashen Duniya Suna Sa Ran Jin Muryoyin Kasar Sin A Taron Kolin G20
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Kaddamar Da Jirgin Ruwa Mai Aikin Nazari A Teku Mai Zurfi
Shugaban ya kara da cewa matukar bangarorin biyu za su mutunta juna, da yi wa juna adalci da kuma cimma matsaya a kan abubuwan da suka sha bamban a kai, tabbas alakar Sin da Australia za ta kara kulluwa.
Ya kuma nunar da cewa, kasar Sin da Australia dukkansu masu goyon baya da kare tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya, da gudanar da ciniki mai ’yanci ne a duniya, kana ya nemi bangarorin biyu su habaka samun damammaki da alfanu a tsakanin kasashe daban-daban ta hanyar kara bude kofa don tabbatar da ci gaba na bai daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)