A yau da yamma ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron da shugabar hukumar gudanarwar Tarayyar Turai EU Ursula von der Leyen a babban dakin taron jama’ar kasar Sin.
A yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya ce, ziyarar hadin gwiwa da shugaba Macron da shugaba Ursula von der Leyen suka kawo kasar Sin, ta nuna kyakkyawar muradin da bangaren Turai ke da shi na raya hulda da kasar Sin, kuma ya dace da moriyar Sin da EU. A halin yanzu, ana fuskantar yanayi mai sarkakiya a duniya, rikicin Ukraine na ci gaba haifarwa duniya kalubaloli, kuma ana fama da karancin karfin farfadowar tattalin arzikin bayan barkewar COVID-19, haka kuma ana fama da girgiza a kasuwannin hada-hadar kudi na kasa da kasa, kasashe masu tasowa na fuskantar karin matsaloli. Kamata ya yi, Sin da EU su nace wajen yin shawarwari da hadin gwiwa, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da sa kaimi ga samun bunkasuwa da wadata tare, da kokarin ci gaban wayewar kan dan Adam, da hada karfi da karfe don tinkarar kalubalen duniya tare.
Daga baya, Xi Jinping da Emmannuel Macron sun halarci bikin rufe taro karo na 5 na kwamitin ‘yan kasuwancin Sin da Faransa tare da ba da jawabi. (Amina Xu)