Yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da firaministan Spaniya Pedro Sanchez, a nan birnin Beijing.
Yayin ganawar, shugaba Xi ya nanata cewa, babu wata nasara da za a samu daga yakin haraji. Ya ce ya kamata Sin da Turai su hada hannu su daukaka dunkulewar tattalin arzikin duniya da kyautata muhallin cinikayya na duniya, da nuna turjiya ga cin zali.
A nasa bangare, Pedro Sanchez ya ce a shirye Spaniya da Tarayyar Turai suke su karfafa tuntubar juna da hadin gwiwa da Sin domin kare muradun bai daya na kasa da kasa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp