Babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da Kim Jong Un, babban sakataren jam’iyyar ma’aikata ta kasar Koriya ta Arewa, kuma shugaban harkokin gudanarwa na kasar Koriya ta Arewa, a yau Alhamis a birnin Beijing. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














