A tsakar ranar yau Lahadi 31 ga wata, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Firayim ministan Indiya Narendra Modi wanda ya zo Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin kan Shanghai (SCO) na shekarar 2025 a birnin Tianjin da ke arewacin kasar Sin.
Shugaba Xi ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata shugabannin biyu sun sami nasarar yin ganawa a birnin Kazan, dangantakar Sin da Indiya ta sake farawa kuma ta ci gaba da samun ci gaba mai kyau. A bana an cika shekarun 75 da kafa huldar diflomasiyya tsakaninsu. Ya kamata bangarorin biyu su hange nesa kan raya dangantakarsu bisa manyan tsare-tsare, kuma kara habaka dangantakarsu mai dorewa yadda ya kamata ta hanyar ganawar Tianjin. Matakan da suka dace wajen karfafa dangantakar sun hada da, da farko, ya kamata a kara tuntubar juna bisa manyan tsare-tsare, da kuma habaka amincewar juna. Na biyu, ya kamata a fadada huldar hadin gwiwa don cin moriyar juna. Na uku, kula da damuwar juna, da kuma nacewa kan yin zaman tare cikin lumana. Na hudu, ya kamata a karfafa hadin gwiwa tsakanin mabambantan bangarori don kare muradun gama gari.
A nasa bangare, Modi ya bayyana cewa, ganawar da ya yi da shugaba Xi a Kazan ta nuna alkiblar ci gaban dangantakar Indiya da Sin, dangantakar ta koma kan hanyar kyau, iyakokin kasashen biyu sun kasance cikin kwanciyar hankali, kuma za a maido da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin kasashen 2 nan ba da jimawa ba. Wadannan nasarorin ba kawai sun amfanar al’ummar Indiya da Sin ba, har ma suna da amfani ga duniya baki daya. Indiya da Sin abokan hulda ne ba abokan hamayya ba, yarjejeniyoyi sun fi bambance-bambance, kuma Indiya tana son yin hangen nesa kan habaka dangantakar kasashen biyu.
Bugu da kari, a wannan rana shugaba Xi ya gana da shugabannin wasu kasashe da suka zo nan kasar Sin don halarar taron, ciki har da shugaban Belarus Alexander Lukashenko, shugaban Azerbaijan Ilham Heydar oglu Aliyev, firayim ministan Armenia Nikol Pashinyan, shugaban Kyrgyzstan Sadyr Nurgozhoevich Japarov, da shugaban Maldives Mohamed Muizzu,da Firaministan Vietnam Pham Minh Chinh kana da shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp