Da safiyar yau Talata 14 ga watan nan na Oktoba, shugaban kasar Xi Jinping ya gana da takwaransa na Ghana John Dramani Mahama a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, wanda ya zo kasar Sin domin halartar taron kolin mata na duniya.
Xi ya bayyana cewa, a bana ake cika shekaru 65 da kafa alakar diflomasiyya tsakanin Sin da Ghana. Ya kuma bukaci bangarorin biyu su tabbatar da sakamakon taron kolin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka na Beijing, tare da binciko hanyoyin hadin gwiwa iri-iri, da fadada hadin gwiwa a fannonin hakar ma’adinai da makamashi da gina kayayyakin more rayuwa, da aikin gona da na kamun kifi.
Ya ce bangarorin sun cimma matsaya daya kan tsai da yarjejeniyar raya huldar abota ta ci gaban tattalin arziki a bangaren samun riba a mataki na farko, kana ya yi fatan Ghana za ta samu fa’ida daga matakin Sin na soke haraji kan kayayyakin dake shiga kasar daga kasashen Afirka masu alaka da ita.
A nasa bangaren, shugaba Mahama ya taya Sin murnar cimma nasarar gudanar da taron kolin mata na duniya. Yana mai cewa taron yana da muhimmanci, kuma ya bayyana karfin jagorancin Sin na daga matsayin ayyukan mata a duniya. Ya ce Ghana tana da dadaddiyar dangantakar abota da Sin, kana ya godewa Sin saboda goyon baya, da taimako da take baiwa mata karkashin taron FOCAC, da kuma shawarar “ziri daya da hanya daya”. Shugaba na Ghana ya yi fatan kara yin hadin gwiwa da Sin a fannonin kasuwanci, da tattalin arzikin dijital, da gina kayayyakin more rayuwa, da kuma makamashi, da hakar ma’adinai da musayar al’adu, domin inganta dangantakar kasashen biyu.
A wannan rana kuwa, shugaba Xi Jinpng ya gana da firaministar kasar Mozambique Maria Benvinda Delfina Levi, wadda take halartar taron koli na mata na duniya dake gudana yanzu haka a birnin Beijing.
Yayin zantawarsu, shugaba Xi ya ce a bana ake cika shekaru 50, da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Mozambique, kuma kawancen gargajiya tsakanin sassan biyu ya jure al’amuran kasa da kasa da dama, yana kuma ci gaba da kasancewa mai karfin gaske.
Ya ce Sin a shirye take ta yaukaka goyon bayan juna tare da Mozambique, da karfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da fadada hadin gwiwar cimma moriyar juna, da ci gaba da zurfafa cikakkiyar huldar kawance daga dukkanin fannoni, da hada hannu wajen raya sabbin shekaru 50 masu zuwa tare.
A nata bangare kuwa, Levy ta ce jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar yayin taron koli na mata na duniya dake gudana, na da matukar tasiri da ma’ana. Kuma Mozambique a shirye take ta yi aiki tare da Sin wajen aiwatar da sakamakon taron, da ingiza ci gaban harkokin mata a matakin duniya.(Amina Xu、Saminu Alhassan)