Da yammacin yau Jumma’a 14 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, wanda har yanzu ke ziyarar aiki a kasar Sin, a babban dakin taron jama’a.
A yayin shawarwarin, Xi Jinping ya yi maraba da ziyarar Lula a kasar Sin. Ya kuma nuna cewa, kasashen Sin da Brazil su ne manyan kasashe masu tasowa, kuma muhimman kasuwanni masu tasowa a gabashi da yammacin duniya, sun kuma kasance abokan hulda bisa manyan tsare-tsare ga juna, kana suna da moriyar juna a fannoni daban daban.
A cewar shugaba Xi, kasar Sin na sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci, da bude kofa ga waje bisa babban matsayi, wanda hakan zai kara samar da damammaki ga kasashen duniya ciki har da Brazil. Kaza lika kasar Sin tana son karfafa yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tare da Brazil, kan batutuwan kasa da kasa dake jawo hankulansu duka, bisa tsarin cudanyar bangarori da dama, ciki har da MDD, BRICS, da G20 da dai sauransu, tare kuma da karfafa hadin gwiwa wajen tinkarar sauyin yanayi.
A nasa bangaren kuwa, shugaba Lula ya bayyana cewa “Wannan ita ce ziyara ta farko a wata kasa da ke wajen nahiyar Amurka, tun bayan da na zama shugaban kasa a wannan karo, wanda ke nuni da irin kaunar da bangaren Brazil ke da shi ga kasar Sin, da kuma muhimmancin da yake ba wa ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, kasarsa ta kuduri aniyar bunkasa huldar kut da kut da kasar Sin bisa matsayin manyan tsare-tsare na sa kaimi ga kafa tsarin kasa da kasa mai adalci da ma’ana.
Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu sun shaida rattaba hannu kan wasu takardu na hadin gwiwa da suka shafi kasuwanci da zuba jari, da tattalin arziki na zamani, da kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, da watsa labarai da sadarwa, da rage talauci, da binciken annoba da kuma sararin samaniya da dai sauransu.
Bugu da kari, bangarorin biyu sun kaddamar da “Sanarwar hadin gwiwa tsakanin Jamhuriyar Jama’ar Sin da Jamhuriyar Tarayyar Brazil, kan zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni.” (Mai fassara: Bilkisu Xin)