• English
  • Business News
Wednesday, September 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping Ya Gana Da Wakilan Da Suka Halarci Taron Tunawa Da Cika Shekaru 60 Da Kasar Sin Ta Fara Tura Ma’aikatan Agajin Jinya Ga Kasashen Waje

by CGTN Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Xi Jinping Ya Gana Da Wakilan Da Suka Halarci Taron Tunawa Da Cika Shekaru 60 Da Kasar Sin Ta Fara Tura Ma’aikatan Agajin Jinya Ga Kasashen Waje
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Kasar Sin Ta Zama Dandalin Karfafa Cudanya Da Cinikayya Tsakanin Kasa Da Kasa

An Kai Jirgin Ceto Na Farko Na Kasar Sin Yankin Tsakiyar Kasar

An yi babban taron tunawa da cika shekaru 60 tun bayan da kasar Sin ta fara aikewa da rukunonin masu samar da agajin jinya zuwa kasashen waje, gami da karrama su a yau Jumma’a 29 ga wata a Beijing, inda babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar, wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin sojan kasar, Xi Jinping ya gana da wakilai mahalarta taron, da taya su babbar murna, da gaisuwa da fatan alheri ga ma’aikatan samar da agajin jinya da a yanzu haka suke gudanar da aiki, ko wadanda suka taba gudanar da aikin a kasashen waje.

Memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne mataimakin firaministan kasar, Liu Guozhong ya halarci ganawar tare da yin jawabi, inda ya ce, kwamitin kolin na maida hankali sosai kan ayyukan samar da agajin jinya a kasashen ketare, kuma shi shugaban kasa Xi Jinping ya yaba matuka da nasarorin da aka samu a wannan fanni. A cikin shekaru 60 da suka gabata, ma’aikatan bada agajin jinyar kasar Sin sun himmatu wajen samar da magani, gami da nuna kauna ga jama’ar kasashe daban-daban, al’amarin da ya sa suka samu babban yabo daga gwamnatoci da al’ummomin kasashen.

  • Za Mu Nome Dazuka Don Magance Matsalar Tsaro A Neja – Bago
  • Kauyukan Yawan Shakatawa Na Sin Na Jawo Hankalin Sassan Kasa Da Kasa

Liu ya ce a sabon zamanin da muke ciki, ya kamata a ci gaba da yayata nagartattun halayen ma’aikatan bada agajin jinyar kasar Sin, da kokarin bude sabon babi ga aikin samar da agajin jinya a kasashen waje, domin kara bada gudummawa ga gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a fannin kiwon lafiya.

Taron ya kuma karrama wasu fitattun rukunonin ma’aikatan bada agajin jinyar kasar Sin 30, gami da wasu daidaikun mutane 60, wadanda suka yi fice wajen aiki. Wakilan wadanda suka samu lambobin yabon sun kuma gabatar da jawabai. (Murtala Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AmurkaJapanSin
ShareTweetSendShare
Previous Post

Za Mu Nome Dazuka Don Magance Matsalar Tsaro A Neja – Bago

Next Post

Xi Jinping Ya Gana Da Jakadun Kasar Sin Dake Kasashen Waje Wadanda Suka Dawo Beijing Don Halartar Taro

Related

Kasar Sin Ta Zama Dandalin Karfafa Cudanya Da Cinikayya Tsakanin Kasa Da Kasa
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Zama Dandalin Karfafa Cudanya Da Cinikayya Tsakanin Kasa Da Kasa

11 hours ago
An Kai Jirgin Ceto Na Farko Na Kasar Sin Yankin Tsakiyar Kasar
Daga Birnin Sin

An Kai Jirgin Ceto Na Farko Na Kasar Sin Yankin Tsakiyar Kasar

12 hours ago
Sin Ta Samu Karuwar Kaso 9.9 Na Sabbin Kamfanoni Masu Jarin Waje A Bara
Daga Birnin Sin

Sin Ta Samu Karuwar Kaso 9.9 Na Sabbin Kamfanoni Masu Jarin Waje A Bara

12 hours ago
Nazarin CGTN: Cin Gajiyar Damarmaki Tare Da Samun Sakamakon Moriyar Juna Ta Hanyar Yin Komai A Bude
Daga Birnin Sin

Nazarin CGTN: Cin Gajiyar Damarmaki Tare Da Samun Sakamakon Moriyar Juna Ta Hanyar Yin Komai A Bude

14 hours ago
Kasar Sin Ta Samar Da Kaso 30 Na Jimillar Kason Ci Gaban Masana’antun Duniya A Tsakanin 2021 Zuwa 2025
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Samar Da Kaso 30 Na Jimillar Kason Ci Gaban Masana’antun Duniya A Tsakanin 2021 Zuwa 2025

14 hours ago
Xi Ya Aike Da Martanin Wasika Ga Wakilan Malamai Na Musamman Don Karfafa Musu Gwiwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Aike Da Martanin Wasika Ga Wakilan Malamai Na Musamman Don Karfafa Musu Gwiwa

17 hours ago
Next Post
Xi Jinping Ya Gana Da Jakadun Kasar Sin Dake Kasashen Waje Wadanda Suka Dawo Beijing Don Halartar Taro

Xi Jinping Ya Gana Da Jakadun Kasar Sin Dake Kasashen Waje Wadanda Suka Dawo Beijing Don Halartar Taro

LABARAI MASU NASABA

Akwai Tara Mai Tsauri Ga Duk Wanda Ya Sare Bishiya Ba Bisa Ƙa’ida Ba – Gwamnatin Kano

Akwai Tara Mai Tsauri Ga Duk Wanda Ya Sare Bishiya Ba Bisa Ƙa’ida Ba – Gwamnatin Kano

September 10, 2025
majalisar kasa

Majalisa Ta Bai Wa Minista Sa’o’i 48 Ya Bayyana A Gabanta Kan Hatsarin Jirgin Abuja Zuwa Kaduna

September 10, 2025
Kasar Sin Ta Zama Dandalin Karfafa Cudanya Da Cinikayya Tsakanin Kasa Da Kasa

Kasar Sin Ta Zama Dandalin Karfafa Cudanya Da Cinikayya Tsakanin Kasa Da Kasa

September 9, 2025
IATF 2025: Zamfara A Shirye Ta Ke Wajen Maraba Da Masu Zuba Jari – Gwamna Lawal 

IATF 2025: Zamfara A Shirye Ta Ke Wajen Maraba Da Masu Zuba Jari – Gwamna Lawal 

September 9, 2025
An Kai Jirgin Ceto Na Farko Na Kasar Sin Yankin Tsakiyar Kasar

An Kai Jirgin Ceto Na Farko Na Kasar Sin Yankin Tsakiyar Kasar

September 9, 2025
Sin Ta Samu Karuwar Kaso 9.9 Na Sabbin Kamfanoni Masu Jarin Waje A Bara

Sin Ta Samu Karuwar Kaso 9.9 Na Sabbin Kamfanoni Masu Jarin Waje A Bara

September 9, 2025
Nijeriya Ta Rasa Tikitin Kai Tsaye Na Zuwa Gasar Kofin Duniya 

Nijeriya Ta Rasa Tikitin Kai Tsaye Na Zuwa Gasar Kofin Duniya 

September 9, 2025
Nazarin CGTN: Cin Gajiyar Damarmaki Tare Da Samun Sakamakon Moriyar Juna Ta Hanyar Yin Komai A Bude

Nazarin CGTN: Cin Gajiyar Damarmaki Tare Da Samun Sakamakon Moriyar Juna Ta Hanyar Yin Komai A Bude

September 9, 2025
Kasar Sin Ta Samar Da Kaso 30 Na Jimillar Kason Ci Gaban Masana’antun Duniya A Tsakanin 2021 Zuwa 2025

Kasar Sin Ta Samar Da Kaso 30 Na Jimillar Kason Ci Gaban Masana’antun Duniya A Tsakanin 2021 Zuwa 2025

September 9, 2025
Rundunar ‘Yansanda Ta Kama Mutum 9 Da Harsasai 4,264 Da Muggan Makamai A Nasarawa 

Rundunar ‘Yansanda Ta Kama Mutum 9 Da Harsasai 4,264 Da Muggan Makamai A Nasarawa 

September 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.