Da safiyar yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, tare da takwarorinsa na Rasha Vladimir Putin, da na kasar Mongoliya Ukhnaagiin Khurelsuh, sun gudanar da taro karo na bakwai na shugabannin kasashen Sin, da Rasha, da Mongoliya a babban dakin taron jama’a dake nan birnin Beijing.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a cikin ’yan shekarun nan, a kai a kai an yi ta samun bunkasar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin, da Rasha da Mongoliya, kuma an samu sakamako mai inganci. An yi nasarar aiwatar da ayyukan hadin gwiwa tsakanin kasashen uku, ana kuma ci gaba da samun bunkasar ciniki a tsakanin kasashen uku, kana ana ci gaba da zurfafa hadin gwiwa a fannonin raya tattalin arziki, da cinikayya, da kimiyya da fasaha, da kare muhalli, da kuma raya al’adu. A matsayin wata makwabtaciyar abokantaka, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Rasha da Mongoliya wajen tabbatar da ainihin burin hadin gwiwa, da kawar da tsoma baki daga waje, da kuma sa kaimi ga bunkasar hadin gwiwa tsakanin kasashen uku.
A nasa tsokaci, shugaba Putin ya bayyana cewa, kasar Rasha tana son yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tare da Sin, da Mongoliya a nan gaba, bisa daidaito da cimma moriyar juna, ta yadda za a sanya hadin gwiwar bangarorin uku da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu su dace da juna, kana kuma su habaka juna.
Shi kuwa shugaba Khurelsuh cewa ya yi, bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin kin hare-haren sojojin Japan da kasar Sin ya gudanar, da babban yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet. Don haka ya kamata al’ummomin Mongoliya, Sin, da Rasha su yi murna, da kuma tunawa da wannan lokaci mai cike da tarihi, da kuma yada madaidaicin ra’ayin tarihin yakin duniya na biyu.
Bugu da kari, a safiyar yau, shugaba Xi Jinping ya gana da firaministan Pakistan Muhammad Shahbaz Sharif, da shugaban kasar Uzbekistan Shavkat Miromonovich Mirziyoyev a nan birnin Beijing.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp