Wata gobara da ta tashi a rukunin wasu gidaje masu yawa, a unguwar Hung Fuk Court da ke yankin Tai Po na gundumar New Territories dake yankin Hong Kong na Sin, ta haddasa asarar rayuka da raunata jama’a da dama.
Bayan aukuwar lamarin, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dora muhimmanci sosai ga al’amarin, yana mai kokarin samun bayanai cikin gaggawa game da ayyukan ceto, da adadin asarar rayuka da gobarar ta haifar.
Shugaba Xi ya kuma umarci babban jami’in ofishin gwamnatin tsakiyar kasar Sin dake yankin Hong Kong, da ya isar da sakon alhininsa ga babban jagoran yankin Hong Kong John Lee, da iyalan wadanda suka mutu a bala’in, da wadanda suka sadaukar da ransu wajen kashe gobarar.
Ya kuma bukaci ofishi mai kula da harkokin Hong Kong da Macao, da ofishin gwamnatin tsakiya dake Hong Kong, da ya tallafa wa gwamnatin yankin Hong Kong da duk abun da ya dace don kashe gobarar, da yin iyakacin kokarin gano da ceton mutane, tare da jinyar wadanda suka jikkata, da ayyukan da za su biyo baya, yayin da sauran hukumomi ke ba da agaji mai mahimmanci, a kokarin rage asarar rayuka da jikkata.
A nata bangare, gwamnatin yankin Hong Kong ta riga ta kaddamar da ayyukan gaggawa na tinkarar bala’in, yayin da ofishin gwamnatin tsakiyar kasar Sin dake Hong Kong ya kafa tawagar gaggawa, don kara tuntubar gwamnatin yankin, da kuma ba da cikakken goyon baya ga ayyukan ceto. (Amina Xu)














