Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tashi daga Beijing da safiyar yau Lahadi, bisa agogon kasar Sin, domin ziyarar aiki a kasashen Faransa da Serbia da Hungary.
Shugaba Xi zai kai ziyarar ne bisa gayyatar da shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban Serbia Aleksandar Vucic da Shugaban Hungary Tamas Sulyok da Firaministan kasar Viktor Orban, suka yi masa.
Tawagar shugaban ta hada da uwargidansa Peng Liyuan da Cai Qi, mamban zaunannen kwamitin ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) kuma daraktan babban ofishin kwamitin kolin JKS, da ministan harkokin wajen kasar Sin kuma mamban ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, Wang Yi. (Mai Fassarawa: Fa’iza Mustapha)