A ranar 8 ga watan Janairu, za a gudanar da cikakken zama na 3 na hukumar koli ta ladabtarwa ta JKS a birnin Beijing, inda za a tsara ayyukan gudanar da mulki na jam’iyya a dukkan fannoni a shekarar 2024.
“Kara karfin jam’iyya don daukar nauyin da ya rataya a wuyanta”wani muhimmin bangare ne na batun cikakken tsarin gudanar da mulki na jam’iyyar, haka kuma wani lamari ne da ba makawa ya dace a samu wajen raya zamanintar da salon mulkin kasar Sin.
A bana za a cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar kasar Sin, da aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, kuma aikin inganta zamanintarwa irin na Sin yana da makoma mai kyau. Kamar yadda babban sakataren JKS Xi Jinping ya ce, sabon matakin yana cike da mutunci da mafarkai, babu gajeren hanya sai aiki tukuru. (Safiyah Ma)