A yau Alhamis ne aka bude bikin baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na Sin, wato CIFTIS na shekarar 2024 a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murnar bude taron mai taken “Baiwa dukkanin duniya hidima da more damammaki masu kyau tare”.
A cikin sakonsa, Xi ya ce, an riga an cimma nasarar gudanar da bukukuwa makamantan wannan har sau 10, kuma hakan ya bayyana inganttaciyar bunkasuwa da aka samu a sha’annin samar da hidimomi, da cinikayya bisa tsarin bude kofa mai zurfi da Sin ke dauka, kuma hakan ya taka rawar gani mai yakini ga kafa tsarin ciniki mai bude kofa a duniya.
- Jihar Kano Ce Za Ta Fara Aiwatar Da Sabon Mafi Karancin Albashi – Gwamna Yusuf
- Nijeriya Na Asarar Dala Biliyan $1.5 Sakamakon Yin Bahaya A Fili
Ya ce Sin za ta ci gaba da nacewa ga gaggauta samun ingantacciyar bunkasuwa bisa tsarin bude kofa a matsayin koli, da ma kyautata tsarin bude kofa ga waje, da kara yin kirkire-kirkire, da daga matsayin ba da hidima, kana da shimfida yanayin ciniki mai kyau dake bin tsarin kasuwanci da oda, da doka, da hadin gwiwa da sassan duniya.
Ya kara da cewa, Sin na fatan kara hadin kai da kasashen duniya, ta yadda za a gaggauta bunkasa tattalin arziki bisa halin da ake ciki na dunkulewar duniya a wannan bangare, da ma taka rawa wajen amfanar da al’umommin duniya baki daya. (Amina Xu)