Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sako jiya Alhamis 28 ga wata, ga Bassirou Diomaye Faye, don taya shi murnar zama shugaban Jamhuriyar Senegal.
A sakon nasa, shugaba Xi ya ce, tun bayan da aka kulla huldar jakadanci tsakaninsu, Sin da Senegal na kara samun fahimtar juna ta fuskar siyasa, da cimma dimbin nasarori a ayyukan hadin-gwiwa, tare kuma da kara goyon-bayan juna a harkokin kasa da kasa. Ya ce a matsayin kasashe shugabannin dandalin FOCAC na bana, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, Sin da Senegal za su hada kai don gudanar da taron kolin FOCAC a kasar Sin a bana.
Kaza lika, Xi ya ce, yana matukar maida hankali kan raya huldodin kasarsa da Senegal, da bayyana fatan yin kokari tare da shugaba Faye, domin kara marawa juna baya, da karfafa hadin-gwiwa, wajen gudanar da taron kolin FOCAC yadda ya kamata, tare da ciyar da dangantakar Sin da Senegal da ma Afirka baki daya gaba, da samar da alfanu ga al’ummun bangarorin biyu. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp