A yau Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sako don taya murnar bude bikin baje kolin kayayyaki na yammacin Sin karo na 20.
A cikin sakonsa, shugaban ya ce bikin ya ba da damar inganta matakin bude kofa ga kasashen ketare da kasar Sin ke aiwatarwa, da zurfafa mu’ammalar shiyyoyi da hadin gwiwarsu, da sa kaimin ci gaban tsare-tsaren masana’antun zamani, gami da samar da dandali na more ci gaban tattalin arzikin yammacin kasar Sin ga kasashe daban daban.
- Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba
- An Kaddamar Da Babban Filin Wasan Da Kasar Sin Ta Gina Wa Kasar Chadi Kyauta
Ban da haka, shugaba Xi ya jaddada cewa, ta hanyar hadin kai ne za a iya tabbatar da ci gaba na bai daya, da moriyar bangarori daban daban. Saboda haka, ana son mai da bikin baje kolin na wannan karo a matsayin damar karfafa fahimtar juna, da kara dankon zumunci, tare da kasashe abokai daban daban, da kare tsarin ciniki da ya shafi mabambantan bangarori masu fada-a-ji, da ingancin tsare-tsaren masana’antu da na samar da kayayyaki na duniya, ta yadda za a ingiza aikin raya tattalin arzikin duniya.
A yau ne aka kaddamar da bikin baje kolin kayayyaki na yammacin Sin karo na 20 a birnin Chengdu na kasar Sin, inda gwamnatin lardin Sichuan na kasar Sin ke karbar bakuncin sa. Jigon taron shi ne “zurfafa gyare-gyare don kara karfi, fadada bude kofa don bunkasa ci gaba”. Taron zai shafe kwanaki 5 ana gudanar da shi, inda ya ja hankulan kamfanoni mahalarta fiye da 3,000 daga kasashe ko yankuna 62 da larduna 27 na kasar Sin.
Baje kolin na bana ya mayar da hankali ne kan inganta manufar hadin gwiwar cinikayya. A karon farko, ya sanya kasashe biyu da kuma larduna biyu su zama masu masaukin baki, wato kasashen Hungary da Laos, da kuma lardunan Zhejiang da Qinghai, kuma Hadaddiyar Daular Larabawa ta kasance abokiyar kawance ta musamman. Ta hakan za a zurfafa dankon zumunci tsakanin lardin Sichuan da kasashe da lardunan da suka gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” tare.
Adadin “nau’i uku na manyan kamfanoni 500” da suka halarci bikin baje kolin a bana ya kai 114, wanda ya kai kashi 55.6 bisa dari. Daga cikin su, akwai kamfanoni 61 dake cikin manyan kamfanoni 500 na duniya, adadin da ya karu da kashi 74.3 bisa dari kan na baje kolin da ya gabata. (Bello Wang, Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp