A yau Jumma’a ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar gudanar da babban taron birane masu sada zumunta na Sin da Amurka karo na 5.
Sakon Xi ya bayyana cewa, al’umma su ne babban tushen raya alakar Sin da Amurka, kuma zumuntarsu ita ce ke taimakawa ga ci gaban alakar. Jihohi da larduna gami da birane da garuruwa masu sada zumunta da juna, muhimman abubuwa ne dake yaukaka zumuncin al’ummomin Sin da Amurka da cimma moriyar juna. Tun da kasashen biyu suka kulla irin wannan zumunci tsakanin biranensu karo na farko a shekara ta 1979, ya zuwa yanzu, jihohi da larduna da birane da garuruwa 284 na Sin da Amurka sun kulla zumunta tsakaninsu. Kuma a wadannan shekaru ke nan, an cimma tudun dafawa wajen zurfafa hadin-gwiwa tsakanin jihohi da larduna da birane da garuruwa na kasashen biyu, al’amarin dake haifar da babban alfanu ga al’ummominsu.
- Sin Ta Yi Kira Da A Hada Kai Wajen Samar Da Tsaron Fasahar AI
- Baje Kolin CIIE Na Kara Jan Hankalin Sassa Kasa Da Kasa
Xi ya jaddada cewa, babban taron birane masu sada zumunta da juna na Sin da Amurka, muhimmin tsari ne na inganta mu’amala tsakanin kananan hukumomin kasashen biyu, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen kara kulla zumunta da fadada hadin-gwiwa tsakanin kasashen biyu. Xi na fatan mahalarta taron za su ci gaba da bada taimako ga kyautata dangantakar Sin da Amurka da kara samar da moriya ga al’ummominsu ta hanyar inganta hadin-gwiwa da sada zumunta tsakanin jihohi da larduna da birane da garuruwa.
An kaddamar da babban taron birane masu sada zumunta da juna na Sin da Amurka karo na 5 a birnin Suzhou na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin a yau 3 ga wata, mai taken “raya birane masu tsabtar muhalli tare, da jin dadin rayuwa tare”. Kungiyar sada zumunta da kasashen ketare ta al’ummar kasar Sin, da gwamnatin lardin Jiangsu su ne suka dauki nauyin shirya taron. (Murtala Zhang)