A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a masana’antar kirkirarriyar basira ta AI dake birnin Shanghai a kudancin kasar Sin, inda ya yi kira ga birnin da ya jagoranci aikin raya fasahar da ma harkokin da suka shafe ta.
Ziyarar na zuwa ne kwanaki 4 bayan shugabannin kasar Sin sun yi wani taron nazarin fasahar ta AI, inda shugaban ya yi kira da a samu fifiko a wannan muhimmin bangare.
Da ya ziyarci cibiyar misali ta kirkire-kirkire ta Shanghai wadda ke zaman mazauni ga kamfanonin sama da 100 dake harkar fasahar AI, shugaban ya ce, fasahar tana samun ci gaba cikin sauri, inda yanzu ta shiga wani gagarumin mataki na bunkasa. (Fa’iza Mustapha)