Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin, ta wayar tarho a yau Jumma’a 8 ga wata.
A tattaunawarsu, Putin ya bayyana ra’ayin kasar Rasha dangane da rikicin Ukraine a halin yanzu, da yadda Rasha ta tuntubi Amurka kwanan nan, inda ya ce, Rasha ta yaba sosai da muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a fannin shawo kan rikici ta hanyar siyasa.
A nasa bangaren kuma, Xi ya jaddada matsayin kasar Sin, tare da bayyana cewa babu wata dabara mai sauki da ke iya magance matsaloli masu sarkakiya. Ba tare da la’akari da duk wani sauyi da za a fuskanta ba, kasar Sin za ta tsaya ga neman sulhu da gudanar da shawarwari. Kazalika, Sin na fatan ganin Rasha da Amurka su rika tuntubar juna, da nufin kyautata dangantakarsu, da taimaka wa warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa.
Har wa yau, shugabannin biyu sun yaba da yadda kasashensu suka amince da juna ta fuskar siyasa da inganta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare, inda suka yarda da kara ciyar da dangantakarsu gaba. Sun ce za su kara hadin-gwiwa da juna wajen gudanar da taron kolin kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO a birnin Tianjin yadda ya kamata, da sa kaimin inganta ci gaban kungiyar. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp