Da yammacin jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi tattaki zuwa birnin Yibin na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar, inda ya ziyarci mahadar wasu koguna uku, da kwalejin Yibin, gami da kamfanin kera kayan laturoni da na samar da wutar lantarki na Jimi, don kara fahimtar yadda ake gyarawa da kiyaye muhallin yankin kogin Yangtze, da samar da guraban ayyukan yi ga daliban da suka gama karatu a jami’a, da harkokin kirkire-kirkire na kamfanoni.
Mahadar kagunan uku ta hada da kogin Yangtze, da kogin Jinsha da na Min a birnin Yibin. Cibiyar wannan wurin na da tsawon kilomita 4.2, da fadin hekta kimanin 73.3, wadda ita ce muhimmin bangare na aikin kiyaye tsaftar muhallin halittu na kogin Yangzte a Yibin, inda ake samar da hidimomin yawon bude ido da al’adu da sauransu ga al’umma. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp