Yau da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci sabon bankin raya kasashen BRICS a birnin Shanghai tare da ganawa da shugabar bankin Dilma Rousseff.
Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata sabon bankin raya kasashen BRICS ya biya bukatun ci gaban kasashe masu tasowa na duniya, da samar da karin kudi ga ayyukan more rayuwa masu inganci da dorewa, da kyautata ayyukan hada-hadar kudi a fannonin kimiyya da fasaha da kiyaye muhalli, da taimakawa kasashe masu tasowa wajen raya fasahohin zamani da canja tsarinsu zuwa mai kiyaye muhalli. Kana a kara yin kokari wajen sa kaimi ga kasashe masu tasowa da su kara bayyana ra’ayoyinsu kan kwaskwarimar tsarin hada-hadar kudi na duniya, da tabbatar da moriyarsu da ba su goyan baya wajen bin hanyar zamanintar da kasa. Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga ayyukan bankin, da kara hadin gwiwa da bankin don mai da hankali kan kiyaye muhalli da yin kirkire-kirkire da kuma samun bunkasuwa mai dorewa, ta yadda za a kara samun nasarori karkashin hadin gwiwarsu.
A nata bangare, Rousseff ta bayyana cewa, a duniya mai cike da tashin hankali, gwamnatin kasar Sin ta tsaya kan tabbatar da moriyar kasashe masu tasowa, da bin ra’ayin cudanyar bangarori daban daban, da tabbatar da adalci a duniya, da sa kaimi ga raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama, da zama abin misali a duniya a wannan fanni. Ta ce bankin zai ci gaba da kokarin samar da gudummawa wajen sa kaimi ga raya kasashe masu tasowa da kasashe masu tasowa wadanda ke da saurin ci gaban tattalin arziki a duniya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp