A safiyar yau Alhamis 24 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron manema labaru na musamman na taron kolin BRICS karo na 15 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu.
Taron ya sanar da cewa, an gayyaci Saudiyya, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Argentina, Iran, da Habasha don zama mambobin kungiyar BRICS a hukumance.
A cikin muhimmin jawabinsa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasashen BRICS kasashe ne dake da babban tasiri, da kuma sauke muhimman nauyin da ya rataya a wuyansu na tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya.
Ya ce, a yayin wannan taro, mun gudanar da tattaunawa mai zurfi kan batutuwan da suka hada da halin da duniya ke ciki, da hadin gwiwar kasashen BRICS, kana mun cimma matsaya guda a fannoni daban daban, da fitar da sanarwar taron koli, ana iya cewa, an cimma nasarori masu yawa.
Baya ga haka, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, shugabannin kasashen biyar sun amince da gayyatar kasashen Saudiyya, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Argentina, da Iran da kuma Habasha, don zama mambobin BRICS. Kasar Sin na taya wa wadannan kasashe murna.
Xi Jinping ya jaddada cewa, aikin fadada mambobin BRICS na da ma’ana a tarihi, matakin da ya nuna aniyar kasashen BRICS na hada kai da kasashe masu tasowa, wanda ya dace da fatawar al’ummomin duniya, tare da biyan bukatun bai daya na sabbin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa da ma kasashe masu tasowa. Har ila yau, ya kasance wani sabon mafari na hadin gwiwar kasashen BRICS, wanda zai sanya sabbin kuzari a cikin tsarin hadin gwiwar BRICS, da kara karfin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya.
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ne ya jagoranci taron, yayin da shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva, da firaministan kasar Indiya Narendra Damodardas Modi da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin wanda ya halarci taron ta kafar bidiyo suka halarci taro.
Taron ya kuma amince da fitar da “Sanarwar Johannesburg ta taron kolin BRICS karo an 15”.
A yayin da yake halartar taron tattaunawa tsakanin shugabannin kasashen BRICS, da kasashen Afirka da sauran sabbin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa da kasashe masu tasowa a birnin Johannesburg, Xi ya nuna cewa, kasarsa ta riga ta kaddamar da wani asusu na musamman na shirin raya kasa na duniya da hadin kan kasashe masu tasowa, a sa’i daya kuma ya bayyana cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana numfasawa kamar kowace kasa tare da raba makoma guda da kasashe masu tasowa, kuma ta kasance, kuma za ta ci gaba da kasancewa mamba a cikinsu har abada. (Mai fassara: Bilkisu Xin)