Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar Xi Jinping, zai duba faretin sojoji da za a gudanar a nan birnin Beijing a kan titin Chang’an ranar uku ga watan Satumba dake tafe.
Babban jami’i a sashen lura da ayyukan hadin gwiwar rundunonin sojoji, karkashin babban hukumar gudanarwar rundunar sojin kasar ta Sin Wu Zeke ne ya bayyana hakan a Larabar nan, yayin taron manema labarai da ya gudana game da shirye-shiryen gudanar da faretin.
Jami’in ya ce za a gudanar da faretin ne a wani bangare na bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yaki da mamayar dakarun Japan da yakin kin tafarkin murdiya. (Saminu Alhassan)














