Gwamnatin tarayya ta kammala shirin kara karbo bashin Dala Miliyan 500 daga Bankin Duniya domin magance karancin ma’aikata a bangaren ilimi da kiwon lafiya a kasar nan.
Bayani ya nuna cewa, ana sa ran amfani da bashin ne domin cike gurbin tsananin rashin ma’aikata a bangaren ilimi da kiwon lafiya a fadin tarayyar kasar nan gaba daya.
- Durkushewar Kamfanoni Ta Kara Rashin Aikin Yi Tsakanin Matasa
- Kudirin Wa’adin Shekaru 6 Ga Shugaban Kasa Ya Tsallake Karatu Na Farko
Kamar yadda kudin bayar da bashin mai suna “Programme Information Document” ya nuna ana sa ran Bankin Duniya ya bayar da amincewarsa a ranar 26 ga watan Satumba 2024, yayin da ma’akatar Ilimi da ma’aikatar lafiya za su jagorancin sanya hannun a bangaren gwamnati.
An tabbatar da za a yi amfani da bashin ne don karfafa bangarorin da isasaun kudi na gudanar da ayyuykansu tare da samar da kwararrun ma’aikata da za su tafiyar bangarorin guda biyu.
Takardar ka’dojin karbar bashin ya nuna cewa, za a tabbatar da amfani da kudaden ne a bangaren inganta daukar kararrun ma’aikata da samar da kayan aiki a dukkan bangarorin biyu.
Wannann yana da matukar mhimmanci in aka lura da cewa, duk jaririn da aka haifa a Nijeriya kashi 36 kacal na abin da ya kamata ya cimma a rayuwarsa yake iya kaiwa gare shi saboda rashin cikakken kiwon lafiya da ilimi.
Kundin ya ci gaba da bayyana cewa, “Nijeriya na fama da rashin kwarrarun ma’aikata a bangaren malamai da ma’aikatan lafiya, in aka kwatanta da sauaran kasashen Afrika tsarararrakinta.