A ranar Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Morocco, wajen goya wa juna baya kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunsu, da kuma sa kaimi ga bunkasa dangantakar Sin da Morocco bisa manyan tsare-tsare.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da yarima mai jiran gado na Morocco Moulay Hassan yayin da ya yada zango a birnin Casablanca bayan kammala ziyarar aiki a Brazil.
- Wasu Gwamnonin Da Ake Hasashen Ba Za Su Koma Kan Kujerunsu Ba A 2027
- ‘Yan Majalisar Nijeriya Na Matsin Lamba Ga Jami’an Gwamnati Wajen Yin Cushe A Kasafin Kudi –Jega
Xi ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Morocco wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka, da taron ministoci karo na 10 na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa, da yin aiki don samar da karin sakamako ta hanyar yin hadin gwiwa a zahiri a fannoni daban daban cikin tsarin hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya.”
A nasa bangaren kuwa, Hassan ya mika sakon gaisuwa da kyakkyawar tarba daga Sarki Mohammed VI ga shugaba Xi, yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da bunkasa yadda ya kamata. Ya kuma gode wa kasar Sin bisa gagarumin goyon bayan da ta baiwa Morocco a lokacin annobar COVID-19, wanda al’ummar Morocco ba za su taba mantawa ba. Ya kara da cewa, iyalan gidan sarauta da gwamnatin Morocco sun kuduri aniyar ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma a shirye suke su ci gaba da yin mu’amala mai kyau da kasar Sin, da karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban. (Yahaya)