Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa ‘yan majalisan Nijereiya na matsinlamba ga jami’an gwamnati wajen yin cushe a kasafin kudi domin cimma burinsu.
Farfesa Jega ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a taron ‘Horar da canjin dabi’un cin hanci da ’, wanda hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuka (ICPC) ta shirya a Abuja.
- Ka Yi Murabus Yanzu Ko Mu Tsige Ka – ‘Yan Majalisa Ga Kakakin Majalisar Bauchi
- Shugaban Majisar Dattawa Ya Yi Wa Daurarru 15 Afuwa Daga Gidan Yari Na Yobe
Ya bayyana cin hanci da rashawa a ma’aikatun gwamnati a matsayin babban cikas ga ci gaban Nijeriya tare da sukar matsalolin da manyan jami’ai ke fuskanta musamman daga bangaren majalisa.
“Akwai mutanen da suke tursasa jami’an gwamnati su gudanar da aikinsu, ko mai kyau ko kuma akasin haka. Wadannan mutane za su iya kasancewa ‘yan majalisa ko kuma ba ‘yan majalisa ba,” in ji shi.
Ya tunatar da yadda wasu ‘yan majalisar suka yi yunkurin yin tasiri a kan kasafin kudi da kuma tabbatar da kwangiloli, wanda hakan ya kawo cikas ga kokarin jami’an gwamnati na tabbatar da gaskiya.
Da yake waiwayar zamansa a hukumar ta INEC, ya bayyana hakan a matsayin za zakaran gwaji dafi ganin yadda ‘yan majalisar ke takurawa kan kasafin kudin hukumar da kwangiloli a kullum.
“Kaurace wa matsinlambar yana bukatar jajircewa. Yana da muhimmanci a kaurace masa don bin bin doka da ka’idojin Nijeriya.”
Ya kuma soki al’adar cin hanci da rashawa da ta yadu a sassan gwamnati tare da yin kira da a sake fasalin hukumomi.
Ana dai zargin majalisar dokokin kasar da cin hanci da rashawa daban-daban da suka hada da karkatar da kasafin kudi na tsawon shekaru. Gudanar da ayyukan mazabu babban misali ne kan hakan.
Wasu rahotannin da hukumar ICPC ta fitar sun bankado yadda ‘yan majalisar dokokin kasar ke amfani da kudaden gwamnati tare da hadin gwiwar hukumomin gwamnati ta hanyar kashe kasafin kudin kasa na ayyukan mazabu wadanda galibinsu ba su ba a aiwatar da su ba.
Rahotannin da ke bin diddigin ayyukan mazabar da ICPC ta fitar sun bankado wasu laifukan da ake zargin ‘yan majalisar tarayya na aikatawa tare da hadin gwiwar wasu jami’an ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya.
Farfesa Jega ya jaddada bukatar samun kwakkwaran jagoranci wajen magance cin hanci da rashawa.
Ya kara da cewa idan ba a samu cikakken sauye-sauye a bangaren shari’a da sauran manyan cibiyoyi ba, cin hanci da rashawa zai ci gaba da wanzuwa. Ya ce al’adar cin hanci da rashawa ta kafu ne ta hanyar lakabin gargajiya da ake ba wa jami’an gwamnati, wanda a ganinsa yana karfafa yin biyayya da ayyukan da ba su dace ba.
“Da zarar an fara yin shit un yana karami, yana ci gaba da girma, ina ba da shawarar sake duba yadda tsarin aikin gwamnati ya tasiri.”
Ya kuma jaddada bukatar karfafa kariya ga masu fallasa bayanan sirri da inganta hanyoyin karfafawa mutane kai rahoton cin hanci da rashawa.
Jega ya bayar da shawarwari da suka hada da kakkarfan kariya ga masu fallasa bayanai, hada kai da matasa, da habaka horar sabbin dabi’un shugabanci.
Da yake goyon bayan bayanan Jega, shugaban ICPC, Musa Aliyu ya bukaci shugabannin ma’aikatun tarayya, sassan da hukumomi da su karfafa tsarin yaki da cin hanci da rashawa.
Ya yi gargadin cewa rashin yin hakan zai sa a gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.
“Ba za a iya kididdiga barnar da cin hanci da rashawa ya yi wa ma’aikatan gwamnati da kuma al’ummarmu ba,” in ji Aliyu, yana mai bukatar jajircewa wajen yaki da cin hanci da rashawa.