A yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, mahukuntan tsakiya suna ba cikakken goyon baya ga Hong Kong wajen daidaitawa da manyan tsare-tsare na kasa da samar da sabon kuzari da fa’ida ga ci gaban tattalin arziki.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da babban jami’in gudanarwa na yankin musamman na Hong Kong(HKSAR) John Lee, wanda ke ziyarar aiki a birnin Beijing. A yayin ganawar, Xi ya saurari rahoto daga Lee kan halin da ake ciki a Hong Kong da kuma ayyukan gwamnatin HKSAR.
Da yake tsokaci cewa, Hong Kong na fuskantar sabbin damammakin samun ci gaba, shugaba Xi ya ce, hukumomin tsakiya za su ci gaba da aiwatar da manufar “kasa daya, tsarin mulki biyu”, da cikakken goyon bayan babban jami’in gudanarwa da gwamnatin HKSAR, wajen hada kai da jagorantar dukkan bangarori na al’umma, da himmatuwa wajen yin gyare-gyare da ci gaba, da kuma neman wadata ta hanyar kirkire-kirkire da kere-kere. (Mohammed Yahaya)