ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Yakin Kasashen Ukraine Da Sudan Suka Janyo Karancin Irin Alkama A Jihar Gombe

by Abubakar Abba
2 years ago
Sudan

Shugaban Kungiyar Manoman Alkama, reshen Jihar Gombe; Lawan Bala Garba, ya bayyana damuwarsa kan yadda yakin da ake ci gaba da gwabzawa a Kasashen Ukraine da Sudan; ke shafar noman Alkama a fadin duniya.

Ya sanar da cewa, yakin ya kuma haifar da karancin samun Iri na Alkama, musamman a Jihar Gombe, wanda hakan ya hana manoma samun damar shuka Irin Alkama, domin noman rani.

  • Bangaren Sin Ya Yi Kira Ga Bangarori Biyu Dake Rikici A Sudan Da Su Yayyafawa Rikicin Kasar Ruwa
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 181, Sun Cafke 203 A Cikin Mako Guda – Hedikwatar Tsaro

Lawan ya ci gaba da cewa, kasar ta  Ukraine ita ce kan gaba a duniya wajen noman Alkamar, amma yakin da ake yi a kasar ya shafi nomanta a Jihar Gombe.

ADVERTISEMENT

Kazalika, ya sanar da cewa; Kasar Sudan wacce ita ma tana kan gaba wajen noman Alkamar a Nahiyar Afirka, yakin da ake yi a kasar ya sanya gaza yin nomanta yadda ya kamata.

A cewarsa, yake-yaken wadannan kasashe biyu, ya haifar da karancin samun Irin Alkamar a duniya, ciki har da  Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Shugaban ya ci gaba da cewa, rashin samun wadataccen Iri na Alkama a kasuwanni, ya haifar da rashin yin noman ranin a bana, duba da kakar noman ranin na bana, na kara karatowa.

A cewarsa, idan manoman ba su samu Irin Alkamar a karshen watan Dismabar 2024 ba, za su yi babbar asara; ko da kuwa daga baya an samu wadataccen Irin Alkamar.

Lawan ya ci gaba da cewa, hauhawar farashin fulawa; ya kara jawo  munanar al’amarin, duba da yadda ake sarrafa Alkamar zuwa fulawa, ba tare da an adana Irin shukarta ba.

A cewarsa, a kasuwannin Jihar Gombe, ba a samu wadatacciyar Alkamar ba, ballatana maganar samun ingantaccen Irinta da za shuka.

Ya yi nuni da cewa, bukatar da ake da ita ta Alkamar ya karu, kuma sauran Irin noman nata da suka yi saura, tuni duk an cinye su.

Sannan, ya bukaci gwamnati ta kawo dauki; musamman wajen samar da wadataccen Irin nomanta.

Shugaban ya kuma bayyana cewa, noman Alkama a Jihar Gombe; na kara zama fitacce, sakamakon yadda ake samun dimbin kudaden shiga daga fannin.

Lawan  ya ci gaba da cewa, sama da manoman Alkamar 9,000 a jihar yanzu; suna noma Alkama a duk shekara; inda Karamar Hukumar Nafada, ta kasance a kan gaba.

A cewar tasa, yanzu a Karamar Hukumar ta Nafada, ana iya yin tunkahon cewa, akwai kadadar noman Alkamar sama da  3,000.

Shugaban ya kuma bukaci manoman jihar, su rungumi dabarun adana Irin Alkamar, mai makon sayar da shi; bayan kammala girbi.

A cewarsa, dole ne manoman su rika gujewa sayar da Irin da suke da shi gaba daya duk da cewa, ana samun makudan kudade idan aka sayar da Irin.

Shugaban ya kara da cewa, gazawar adana Irin; zai jawo musu gagarumar matsala a kakar noma ta gaba.

Lawan ya kuma jaddada muhimmancin gwamnati, wajen kawo daukin gaggawa; domin ganin yadda noman Alkamar ke kara lalacewa a yankin.

Sudan
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Next Post
Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yi Watsi Da Ƙara A Kan LEADERSHIP

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yi Watsi Da Ƙara A Kan LEADERSHIP

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.