Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi ga mahalarta liyafar maraba, da shi da mai dakinsa suka shiryawa manyan baki da suka iso kasar Sin, don halartar taron tattauna hadin kan Sin da kasashen Afirka ko FOCAC na 2024.
A cikin jawabin nasa a yau Laraba, shugaba Xi ya ce a baya da kuma yanzu, Sin da kasashen Afirka sun zamo sassa na farko da suka gina al’umma mai makomar bai daya, kuma tabbas za su hada hannu wajen zama sahun gaba a turbar zamanantarwa a nan gaba.
- An Gudanar Da Taron Ministoci Na Dandalin FOCAC Karo Na 9 A Beijing
- Za A Nuna Shirin Talabijin Na Gaskiya Mai Taken “Ciyawar Kasar Sin” A Tashar CCTV-4
Shugaba Xi ya yi imanin cewa, muddin al’ummun Sin da na Afirka biliyan 2.8 sun yi aiki tare, ba shakka za su cimma nasarar samar da sahihiyar hanyar zamanantarwa, da ingiza ci gaban hakan tsakanin kasashe masu saurin ci gaba da masu tasowa, tare da ba da babbar gudummawa ga gina al’ummar bil adama mai makomar bai daya.
Da yammacin yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da mai dakinsa Peng Liyuan suka jagoranci liyafar maraba da zuwan manyan baki mahalarta taron tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ko FOCAC na 2024, a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing. Daya sun dauka hoto tare. (Mai fassara: Saminu Alhassan)