Babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja, Xi Jinping, wanda ya jagoranci tawagar wakilan kwamitin kolin JKS don halartar bikin cika shekaru 60 da kafuwar yankin Xizang mai cin gashin kansa na kasar Sin, ya saurari rahoton ayyuka daga kwamitin JKS da gwamnatin yankin Xizang mai cin gashin kansa yau Laraba.
Ya jaddada cewa, dole ne yankin Xizang ya aiwatar da dabarun JKS na gudanar da mulkin yankin a sabon zamani, da bin ka’idar neman ci gaba cikin kwanciyar hankali, tare da aiwatar da sabon tsarin ci gaba, da sa kaimi ga samun bunkasa mai inganci, da ci gaba da kula da manyan batutuwa guda hudu wato kwanciyar hankali, da samun habaka, da inganta muhalli, da karfafa yankin kan iyakar kasa, ta yadda za a gina yankin Xizang mai salon zamantarwa na tsarin gurguzu wanda ke da hadin gwiwa, arziki, wayewar kai, daidaito, da kuma kyakkyawan yanayi.(Safiyah Ma)














