Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murnar kammala da fara aikin tashar Qinling dake yankin Antatika.
A jiya ne dai, tashar Qinling,dake zama tashar bincike ta biyar ta kasar dake Antatika ta fara aiki.
Ya bayyana cewa, a bana ne ake cika shekaru 40 da kasar Sin ta fara gudanar da aikin bincike a yankin Antatika. Yana mai cewa, sakamakon binciken da kasar ta gudanar a fannin teku, ya samu sakamako mai kyau, kuma kammala aikin gina tashar Qinling zai ba da tabbaci mai karfi ga masana kimiyya na kasar Sin da ma duniya baki daya, don ci gaba da yin binciken abubuwan ban alajabi gami da jajurcewa a kololuwar binciken kimiyya. (Ibrahim Yaya)