A jiya Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sako ga Dharam Gokhool don taya shi murnar kama aiki a matsayin shugaban kasar Mauritius. Yana mai bayyana cewa Mauritius muhimmiyar abokiyar hulda ce ta kasar Sin a Afirka, kuma an daukaka huldar dake tsakanin kasashen biyu zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tare da hadin gwiwar bangarorin biyu.
Xi ya kara da cewa, yana mai da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da Gokhool, wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a Beijing, da kara amincewa da juna a fannin siyasa, da fadada hadin gwiwa a aikace a fannoni daban-daban, da ingiza bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp